Sabon maganin ya kashe sama da kashi 99% na kwayar cutar a cikin makonni biyu, kuma yana yiwuwa yafi maganin da ake amfani da shi a hanlin yanzu kaifi.
Wannan ci gaban da aka samu, ya kara ba kwararru karfin guiwar cewa, suna dab da samun rikagafin cutar, musamman ganin yadda cutar take nuna alamar kin jin magani, yayinda binciken ya kuma nuna cewa, amfani da maganin yana rage tsawon jinya da kimanin shekara daya.
Sakamakon binciken da aka bayyana a wurin taron yaki da cutar kanjamau na kasa da kasa da aka gudanar a birnin Washngton DC ya kuma nuna cewa an sami ci gaba a kokarin samar da maganin rage kaifin cutar kanjamau da yake tafiya kafada da kafada da jinyar tarin fuka, wanda yake da muhimmanci wajen jinyar masu tarin fuka da suke dauke da kwayar cutar kanjamau.
Tarin fuka da cutar kanjamau sune cututukan da ke kan gaba wajen kashe mutane a duniya, sai dai sau da dama ba a iya jinyarsu a lokaci daya sabili da illar da ke akwai idan aka yi amfani da magungunan a lokaci daya.