Kawo yanzu kimanin kaji dubu talatin da takwas ne ma'aikatar gona a jihar Filato ta hallaka.
A cewar jami'in dake kula da cutar masassarar tsuntsaye a jihar Filato Dr. Haruna Ayuba ya zuwa yanzu manyan gonaki takwas ne lamarin ya shafa inda suka kashe kajin suka kuma binnesu kana suka fesa feshin hana yaduwar cutar.
Ma'aikatan sun jawo hankalin masu gonakin da su dinga kula da yadda mutane ke shiga da fita daga gonakinsu domin kiyaye sake yada masu cutar. Da zara sun lura da faruwar wani abu an gargadesu su sanarda ma'aikatar cikin gaggawa.
Shugaban kungiyar masu kiwon kaji ta jihar Mr. John Dafar yace suna fadakar da 'yanuwansu mahimmancin tsafta a gonakinsu. Yace tun shekarar 2015 zuwa yanzu sun yi hasara kaji fiye da miliyan daya. Idan aka kwatanta hasarar da kudi ta fi nera biliyan daya.
A kungiyance sun ba kansu shawara su yiwa gonakinsu inshora domin rage hasara tunda gwamnati bata taimakonsu idan an samu barkewar cutar kaji.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.