Ministan Ma’aikatar Lafiya na Najeriya Dr. Osagie Ehanire ya tabbatar da samun karin wasu mutum 5 dake dauke da cutar coronavirus a Najeriya. A wata hira da yayi da manema labarai a birnin Abuja, ya ce a birnin Legas aka gano mutanen su biyar.
Cikin mutanen 5, akwai wani dan Amurka da ya shigo kasar daga iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin. Sauran kuma ‘yan Najeriya ne, ciki har da wani karamin yaro da mahaifiyarsa da suka zo daga Amurka, sai kuma wasu maza su biyu da suka dawo kasar daga Birtaniyya.
Yanzu dai adadin masu dauke da wannan cuta a Najeriya ya kai mutum 8 kamar yadda ministan ya bayyana.
Tun da farko dama gwamnatin Najeriya ta bada sanarwar tsagaita zirga
zirga tsakanin Najeriya da kasashen da cutar ta yi kamari irin su China, Italiya, Spain, Koriya ta Kudu, Amurka da kuma Birtaniya har zuwa nan da makwanni 4.
Dama kafin daukar wannan matakin Majalisar Dattawan kasar ta yi kira ga
gwamnati da ta tsaigaita zirga zirga. Hakazalika ita ma kungiyar likitoci ta kasa ta yi irin wannan kiran dake neman a hana jiragen kasashen waje sauka Najeriya domin rigakafin cutar ta coronavirus.
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta fidda sanarwar rufe sansanonin horar da ‘yan yiwa kasa hidima da kuma dakatar da wasannin kasa na shekara-shekara, duk a matsayin rigakafin bazuwar cutar coronavirus.
Ga karin bayani cikin sauti.