A Najeriya gwamnatin jihar Bauchi ta samar wa mata fiye da dubu biyar aikin girkin abinci a makaratun firamari, awani shirin gwamnatin tarayya Najeriya na tallafawa marasa karfi. Ga Abdulwahab Muhammad ga Karin bayani.
Jami’I mai kula da shirin a jihar mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi, a fanin aiyukan gwamnatin tarayya da kungiyoyi Alhaji Manu Soro Mansur, yayi bayanin cigaban da aka samu a fanin tattalin arziki da na ilimi a sanadiyar shirin.
Yana mai cewa gaskiya an samu cigaba a jihar Bauchi,sanadiyar wannan shiri na ciyar da dalibai kuma jihar ce na biyu a yawan yaran da ake ciyarwa yace a kwai fiye da yara dubu dari biyar da.
Ya kara da cewa wannan shiri yasa an samu Karin kashi arba’in cikin dari na dalibai da suke zuwa makaranta, kuma akwai makarantu fiye da dubu biyu da ake ciyarwa a jihar ta Bauchi.
A gefe guda kuma matar gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abubakar, ta kaddamara da shirin baiwa matan da aka dauka aiki situran aiki da katin sheda domin inganta tsarin shirin a jihar ta Bauchi.
Facebook Forum