Rundunar ‘yan Sandan jihar Borno, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane hudu sakamakon tashin wasu boma bomai, da ya afku a garin Maiduguri.
Kwamishinan ‘yan Sanda Mr. Chukwu, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, yace an saka tashi da wani abun takaishi inda aka samu tashin a garin Maiduguri.
Yace da misalign kafe goma zuwa goma sha biyun daren jiya ne dai aka samu kunar bakin wake na farko, a wani kauyw da ake kira Usmanti, da yake kokarin haurawa zuwa cikin garin Maiduguri, yayinda Sojojin dake tsaro a wanna yanki suka bude masa wuta inda bom din ya tashi dashi kuma yam utu shi kadai.
Ya kara da cewa ko a yau da safe wasu ‘yan kunar bakin waken sunyi kokarin shigowa cikin garin Maiduguri, ta yankin da ake kira Kaleri, da misalin karfe biyar saura minti goma inda wata ta tayi kokarin tsallakawa kan iyakar da aka tsaga kafin wasu jami’an Sojoji, dake aikin sintiri a yankin suka hango ta suka ko bude mata wuta da bisani jami’an ‘yan Sanda suka kwance bom din domin bai tashi ba a lokacin da aka harbe ta.
Kwamishinan ‘yan Sandan, yace amma daya daga ckin wadannan ‘yan kunar bakin waken ta samu ta tsallake shingen jami’an tsaron wanda kuma tayi kokarin shiga cikin gari, kimanin kusan mita dari biyu ne daga shingen ta tada bom dinta wanda yayi sanadiyar mutuwar wani mutu da kuma raunata wasu mutane biyu.