WASHINGTON DC - A yau Talata ne, aka rantsar da sabon zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye
Shugaba Faye ya yi nasara da kashi 54 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben a kan abokin hamayyarsa na hadakar jam'iyyu masu mulki.
Ranar Juma'a ne Kotun Kolin Kasar ta tabbatar da nasararsa a zaben da aka gudanar ranar 24 ga watan Maris 2024.
A jawabinsa na farko a matsayin zababben shugaban kasa, Faye ya yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa da kuma gyara tattalin arzikin kasar.
Shugaba Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), zai bi sahun sauran shugabannin kasashen yankin domin halartar bikin a cibiyar Diamniadio Exhibition Centre.
Ministan harkokin wajen kasar Yusuf Tuggar da wasu manyan jami'an gwamnati ne zasu raka shi a wannan ziyarar.
Dandalin Mu Tattauna