Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Moctar Ouane a Matsayin Firai Ministan Mali


Firai Ministan Mali MOctar Ouane
Firai Ministan Mali MOctar Ouane

An nada tsohon Ministan Harkokin Wajen Mali, Moctar Ouane, a matsayin Firai Ministan kasar da ke yammacin Afirka, yayin da take kokarin maida  al’amuranta daidai, bayan da aka hambarar da gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita a watan da ya gabata. 

Shugaban gwamnatin rikon kwarya, Bah N’Daw, wanda kwamitin sojojin da ke mulkin kasar suka nada ranar Juma’ar da ta gabata ne ya nada Ouane a matsayin Firai Minista a jiya Lahadi yayin da shi kuma wanda ya jagoranci juyin mulkin, Kanal Assimi Goita ya zama mataimakin Shugaban kasa.

Ouane, ya yi aiki a matsayin ministan harkokin waje daga shekarar 2004 zuwa 2011, bayan da ya wakilci Mali a matsayin jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya daga shekarar 1995 zuwa shekarar 2002.

Ta yiwu nadin Ouane a matsayin Firayim Minista ya kai ga janye takunkumin da kungiyar kasashen ECOWAS ta kakaba wa Mali bayan da dakarun sojin kasar suka kama Keita dan shekaru 75, da kuma Firayim Ministan sa a lokacin Boubou Cisse a ranar 18 ga watan Agusta a gidan Keita da ke Bamako babban birnin kasar.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG