A watan Afrilu da ya gabata ne, wani kwamiti daga cikin kungiyar Tarayyar Afirka ya bada shawarar fitar membobin Kungiyar daga kotun ta duniya ko ICC a Turance, har sai an yarda da sharrudda guda uku. Daya daga cikin sharruddan shine, bada kariyar da zata hana gurfanar da shugabannin kasashen Afirka, tare da wasu masu rike da manyan mukamai har sai sun sauka daga mukamansu.
Kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch dake da matsuguni a nan Amurka ce ta jagoranci tawagar kungiyar, inda suka bayyana bada kariya ga shugabannin kasashen Afirka ya sabawa Kundin tsarin kungiyar Tarayyar Afirka, haka kuma ya yi hannun riga da damarar murkushe rashawa da kungiyar ta Tarayyar Afirka ke son yi.
Kungiyoyin kare hakkin sun ce, baiwa shugabannin Afirka kariya baya cikin tsare-tsaren Kotun Duniya, sannan fitar da mambobin Kotun a barshi a hannun kasashen akan kansu.
A gobe Juma'a ne wakilan Kungiyar Tarayyar Afirkan zasu zauna tattauna a zauren tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, donwannan batu.