Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Dalibai 29 A Makarantar Sakandare ta Mamudo, Jihar Yobe


Gwamnan jihar Yobe ya ziyarci wadansu da aka kaiwa hari a jihar
Gwamnan jihar Yobe ya ziyarci wadansu da aka kaiwa hari a jihar

Yan bindiga sun kashe dalibai 29 da malami daya a wata makarantar sakandare ta kwana dake garin Mamudo a jihar Yobe.

Wadansu ‘yan bindiga sun kashe a kalla dalibai 29 da malami daya a wata makarantar sakandare ta kwana, bayan sun cinnawa gine ginen wuta suka rika harbin dalibai dake kokarin ceton rayukansu.

Wadanda suka tsallake rijiya da baya sunce an kone wadansu kurmus da ransu jiya asabar a wani harin da aka kai da asuba a kauyen Mamudo dake arewa maso gabashin Najeriya da ake fama da tashe tashen hankali. Wani dalibi yace an tashe shi da bindiga, aka kuma harbeshi aka ji mashi rauni, aka tsinke yatsunshi hudu na dama. Dalibai da dama kuma sun gudu suka shiga jeji, ba a kuma san makomarsu ba.

Makarantar tana yankin da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci ya kuma tura dakaru da nufin shawo kan tada kayar bayan da mayaka ke yi na neman kafa shari’ar Islama.

Sai dai wani mutum da ya rasa ya’yanshi biyu a harin yace babu tsaro a yankin. Yace ‘yan bindiga suna kaiwa makarantu hari kuma ba a kare dalibai duk da sojojin dake ke wurin.

Hukumomi suna kyautata zaton kungiyar Boko Haram ce ta kai harin.

Wakiliyarmu Sa’adatu Mohamad Fawu tayi hira da wani mazaunin garin Mamudo dangane da harin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:48 0:00
Shiga Kai Tsaye
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG