Wani harin da aka kai kan farar hula a gandun shakatawa na kasa mai suna Virunga a Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo, ya yi sanadin mutuwar mutane 18, ciki har da dogarawan kula da dajin 12.
Virunga na cikin rakunin wuraren da hukumar kula da harkokin kimiyya da ilimi da al’adu ta duniya ta UNESCO ta ayyana a matsayin wuraren tarihi na duniya. Wurin, wanda ke da fadin kilomita 7,800 kilomita murabba’i, na shinfide ne a wuraren da Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo ta yi iyaka da kasashen Rwanda da Uganda.
Shi ne wuri mafi dadewa kuma wanda ya kunshi halittu daban daban a jerin wuraren da hukumar UNESCO ke karewa.
Gandun dajin, wanda ke kunshe da dinbin nau’ukan goggon birai masu zama kan tsauni, ya kasance wurin da ake dada takaddama a kansa da kuma munanan tashe tashen hankula na tsawon a kalla shekaru 20.
An hallaka 176 daga cikin dogarawan tsaron gandun dajin cikin shekaru 20 da su ka gabata a hare haren da kungiyoyin ‘yan tawaye, da ‘yan bindiga da masu farauta ba bisa ka’aida ba su ka kai.
Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin na ranar Jumma’a.
Facebook Forum