Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe mutane 17 a wasu hare-hare kan Majami'u a kasar Kenya


Wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su
Wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su

‘Yan sandan Kenya sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wasu majami’u biyu a garin Garissa da ke gabashin kasar a jiya Lahadi

‘Yan sandan Kenya sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wasu majami’u biyu a garin Garissa da ke gabashin kasar a jiya Lahadi, su ka hallaka mutane 17 tare da raunata wasu akalla 40.

Hukumomi sun ce maharan sun jejjefa gurneti sannan su ka bude wuta kan masu ibada.

Wannan mummunan harin an kai shi ne kan Majami’ar African Inland Church, inda mutane akalla 10 su ka hallaka, ciki har da ‘yan sanda biyu. Hari na biyu ya auku ne a wata Majami’ar Katolika.

Babu wanda ya dau alhakin kai harin nan take. A baya ‘yan sanda sun zargi wasu masu alaka da kungiyar Islama ta al-Shabab da ke kasar Somaliya da laifin kai hare-hare. Kenya ta tura dakarunta cikin kasar Somaliya a bara don su taimaka wajen farauto ‘yan bindigar al-Shabab. ‘Yan gwagwarmaya da makamin na so ne su mai da kasar Somaliya tsattsaurar kasar Islama.

Fadar Shugaban Amurka ta White House, ta yi Allah wadai da hare-haren da kakkausan harshe, tare da aikawa da sakon matukar ta’aziyyarta ga iyalan wadanda abin ya rutsa da su. Ta ce maharan ba su darajanta ran dan adama kuma ba su mutunta mutum, don haka dole ne a fuskanci hukunci.

XS
SM
MD
LG