Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mayakan AL-shabab 18 a Wani Harin Jirgin Sama a Somaliya


Sojojin sSomaliya a kusa da Barawe, Somalia, Oct. 4, 2014.
Sojojin sSomaliya a kusa da Barawe, Somalia, Oct. 4, 2014.

Babu wani sojan Amurka ko na kawayenta Somaliya da ya sami ko da rauni a harin da yayi sanadiyyar kashe mayakan Al-shabab 18 a Somaliya.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito cewae sojojin Amurka sun ce sun kai wani harin jirgin sama a matsayin kare kai da yayi sanadiyyar mutuwar yan kungiyar ta’adda ta Al-Shabab 18 bayan wani shirin kai hari da akai wa dakarun Amurka da na kasar a kudancin Somaliya.

Kwmandan dakarun Amurka a Afirka ya fada a wani rubutaccen bayani cewa an kai wannan hari ne a matsayin kare kai a ranar Juma’a, Kilomita 50 a Arewa maso yammacin birnin gabar teku na Kismayo.

Jawabin yace sojojin Somaliya sun kashe biyu daga cikin yan ta’addar na Al-shabab ne da kananan bindigogi a yayin kai harin.

Mai magana da yawun dakarun na Amurka a Afirka ya ce babu wani soja na Amurka ko na kawayenta da ya ji rauni, haka kuma an kai harin ne yayin da aka ga yan ta’addan na shirye shiryen kwanton bauna a wurin da sojojin Amurka da na Somaliya ke sintiri.

Amurka ta kaddamar da ire iren wannan hari 20 a wannan shekarar akan abokanan na Al-kaida wato Al-shabab, kungiyar da ta kasance mafi hadari a cikin kungiyoyin yan ta’adda da ke kudancin saharar Afirka.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG