Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Jamian Aikin Wanzar Da Zaman Lafiya Su Hudu Dake Aiki A Mali


Afghanistan,Suicide attack in Kandahar Khos Aab area in Romania soldiers, 15.sep2017
Afghanistan,Suicide attack in Kandahar Khos Aab area in Romania soldiers, 15.sep2017

An kaiwa jamian wanzar da zaman lafiya naMajilisar Dinkin Duniya hari a kasar Mali, kuma an hallaka mutane 4 daga cikin su da kuma sojan Mali guda.

Tawagar samar da zaman lafiya na MDD dake kasar Mali tace jamian ta 4 da sojan kasar Mali 1 aka hallaka a jiya jumaa a wasu hare-hare guda biyu da aka kai, kana mutane 21 ne suka samu rauni.

Farhan Haq mukaddashin mai Magana da yawun Sakataren MDD ya fada cewa, wannan harin ba shine na farko ba domin jamian sun samu nasarar kassara wani yunkurin harin da akayi kokarin kai musu, duk da yake dai jamiian wanzar da zaman lafiya sunyi hasarar rayukan su a yankin Manaka.

Haq yace sakataren na MDD Antionio Guteres yayi ALLAH waddarai da wannan harin.

Mai Magana da yawun Sakataren yace harin da ake kaiwa masu aikin wanzar da zaman lafiya wannan tamkar kwatankwacin laifin yaki ne a karkashin dokokin kasa da kasa kuma ana iya wa wanda aka samu da aikata wannan hukuncin yaki.

Kwamitin samar da zaman lafiya na MDD yace za a samar da wani sabon rundunar soja daga kasashen dake yankin Sahel, da suka hada da Mali,Niger,Bukina Faso,Murtania da Chad, domin su samar da zaman lafiya a yankin

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG