An gudanar da addu'oi ga ‘yan matan Najeriya 26 wadanda suka mutu a yayin da suke kokarin ketara tekun maliya a yau jumma,a garin Salerno dake kusa da Naples a kudanci kasar Italiya . Malaman addinin kirista da na Islama ne suka jagoranci addu’oin.
A rahoton da wani mai gani da ido ya bayar, yace akwatinan gawa 26 aka rufe a tsohuwar makabartar garin Salerno a ranar jumma’a da safe inda suka samu halartar jami’an tsaro ‘yan siyaysa, ma’aikatan agaji da kuma ‘yan jaridu da dama.
Kowanne akwatin gawa yana dauke da farar fulawa a saman shi illa guda biyu da suke dauke da sunayen Marian Shaka da Osato Osaro.
Rahotanni sun bayyana cewa za’a binne su ne a makabartu daban daban.
An kuma ware ranar jumma’ar da ta zama ranar makoki a garin kuma makarantu sun dauki minti daya na yin shiru haka zalika za’a kashe fitulu dake manyan gurare domin tunawa da mutuwar ‘yan matan.
A cewar rahoton, gawawwakin sun iso garin Italiya ne a ranar 3 ga watan Nuwamba bayan da aka samo su a teku. An gudanar da bincike akan dalilin mutuwarsu kuma an samu sakamako cewa 25 daga ciki ruwa ne ya shanye su 1 kuma ta samu rauni daga gefen ta . an kara da cewa daukacin matan yan asalin Najeriya ne yan shekaru 14 zuwa 30 , biyu daga cikin su suna dauke da juna biyu harda Osaro wacce ke dauke da ‘yan biyu, sabili da haka ne aka saka fulawoyi biyu akan akwatin gawarta masu kalar shudi da ja, domin tunawa da su.
A kalla mutane 100 daka cikin ‘yan tawagar tasu sun bace kuma ana kyautata zaton suma ruwa ne ya tafi dasu .
Wani jirgin sojojin spain ya yi nassarar tseratar da a kalla mutane 400 da kuma gano gawawwaki 26 a yankin Sicily a farkon watan Nuwamba. Suna kokarin tsallakawa daga Libya zuwa Italy a lokacin da jiragen ruwan da suke ciki suka kife, amman rahoton da aka bayar bai nuna cewa akwai ‘yan Najeriya a ciki ba.
Facebook Forum