Domin tabbatar da an yi zabe mai inganci a zaben cike gurbi da za'a yi a kudancin jihar Bauchi Asabar din nan, hukumar zabe ta INEC ta shirya tsaf dominzaben, saboda haka ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki.
Wadanda INEC ta yi taron dasu sun hada da jami'an tsaro da shugabannin jam'iyyun siyasa, da kuma 'yan jarida.
Kwamishanan 'yan sanda dake kula da ayyukan zabe na hedkwatar ofishin 'yan sanda a Abuja Ahmed Iliyasu, ya bukaci 'yan siyasa da su ba da hadin kai ga jami'an tsaro domin gudanar da aikin zaben saboda a sami nasara.
Ahmed Iliyasu ya kira hadin kan kowa, da duk wadanda suke da hannu a zaben tare da kiran duk wadanda abun ya shafa su bi doka. Kiyaye doka ne zai sa ayi zaben cikin kwanciyar hankali, walwala da lumana. Ya ce ba zasu lamunce da duk wanda zai kawo tashin hankali ba.
Hukumar zaben shiyyarta dake jihar Bauchi, ta bakin jami'inta dake hulda da jama'a Muhammad Yahaya Salihu, ya ce akwai ma'aikatan zabe su dubu uku da zasu yi aiki a rumfunan zabe 1,900 ranar Asabar idan Allah Ya kai rai.
Za'a fara zaben daga karfe takwas na safe har zuwa karfe hudu na yamma.
Wasu wakilan jam'iyyun siyasa sun nuna gamsuwa da shirin zaben amma sun kira a tabbatar da gaskiya tare da tura kayan aikin zabe akan lokaci.
Mahmud Baba Maji sakataren wata jam'iyya ya ce ya ji dadi da yadda hukumomin tsaro da na zabe suka tara duk masu ruwa da tsaki akan zaben. Ya ce su abun da suke bukata ke nan daga bangaren jami'an tsaro.Shi ko Ahmed Salisu Barau na jam'iyyar Green Party, ya godewa Allah da ya sa hukumar zabe ta kira taron da fatan zasu zama masu adalci. To sai dai Ahmed ya yi korafin cewa wasu 'yan siyasa suna yawo suna sayen katin zabe akan Nera dubu biyar. A cewarsa kowa ya san da haka a jihar Bauchi.
A saurari rahoton Abdulwahab Muhammad domin karin bayani
Facebook Forum