Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Ma'aikatan Jinya a Zimbabwe Bayan Sun Fito Zanga-zanga


'Yan sanda a lokacin wata hatsaniya bayan da likitoci suka fito zanga-zanga kan karancin albashi a shekarar 2019, a kasar Zimbabwe.
'Yan sanda a lokacin wata hatsaniya bayan da likitoci suka fito zanga-zanga kan karancin albashi a shekarar 2019, a kasar Zimbabwe.

'Yan Sanda a Zimbabwe sun kama ma'aikatan jinya 12 wadanda suka fito zanga-zanga a wajen asibitocin gwamnati.

Kungiyar ma;aikatan jinya ta kasar ta ce sun fito zanga-zanga ne domin bukatar a biya su albashi da kudin dalar Amurka yayin da hauhawar farashin dala ke yi wa albashinsu illa.

Wani ma'aikacin Reuters ya shaida yadda 'yan sanda a birnin Harare suka kama wasu ma'aikatan. Mai magana da yawun 'yan sanda a kasar, Paul Nyathi ya ce bai da masaniya kan lamarin.

Ma'aikatan wadanda suka fito rike da kwalayen da aka rubuta "babu dala, babu aiki" da kuma "ma'aikata basa iya numfashi" sun ce sun fito zanga-zanga ne saboda bayyana yadda ba za su iya rayuwa da albashin dalar Zimbabwe 3000 ba.

Yadda ma'aikatan jinya suka fito zanga-zanga a shekarar da ta gabata bayan da aka sace wani dan uwansu.
Yadda ma'aikatan jinya suka fito zanga-zanga a shekarar da ta gabata bayan da aka sace wani dan uwansu.

A cewar wata mata a wurin zanga-zangar, "ba zan zauna ina aikin banza ba, dole sai na ci abinci saboda in iya yin aiki na da kyau."

Zanga-zangar wacce ta faru a wurare daban-daban, ciki har da asibitin Zimbabwe mafi girma da ke birnin Harare, na faruwa ne a lokacin da Covid-19 ke kara kama mutane a kasar.

Ya zuwa yanzu dai mutane akalla 716 ne ke fama da cutar, yayin da takwas suka rasa rayukansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG