Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Da Ake Zargi Da Safarar Tabar Wiwi a Nijar


Mutanen da aka kama bisa safarar tabar wiwi a Nijar
Mutanen da aka kama bisa safarar tabar wiwi a Nijar

Jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Nijar sun yi nasarar cafke wasu mutane 7 dauke da daruruwan kilogram na tabar wiwi hade da miliyoyin cfa da aka boye a wata trela.

Kimanin kilo 240 na tabar wiwi da aka nade a sinki-sinki ne hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato OCRTIS ta kama a hannun wasu diloli wadanda dubunsu ta cika bayan da ‘yan sanda suka gudanar da binciken kwakwaf a watan babbar motar daikon kaya

Mataimakiyar darektan hulda da jama’a a hukumar ‘yan sanda ta kasa kwamishiniya Nana Aichatou Ousmane Bako ta yi wa Muryar Amurka karin bayani a lokacin da aka gabatar da wadanan diloli a gaban manema labarai.

“Kwayar da suke dauke da ita sai da ta ketare wajen kasa uku kafin aka gano su a yanzu.”

A cewar Bako “sai wanda ya san aikinsa zai iya gane wadannan kwayoyin bisa yadda suka boyesu.”

Trelar da suka yi amfani da ita
Trelar da suka yi amfani da ita

Babban alkali mai tuhuma Procureur de la Republique da mukarrabansa sun ziyarci ofishin hukumar ta OCRITIS domin jinjinawa ma’aikata sakamakon gamsuwa da nasarorin da suke samu.

“Safarar miyagun kwayoyi haramtaciyar sana’a ce da duniya ta tanadi hukunci mai tsanani akan duk wanda ya jefa kansa cikin wannan danyen aiki” inji Procureur Maman Tsayabou Issa.

Kudade da kuma wayoyin masu safarar tabar wiwin
Kudade da kuma wayoyin masu safarar tabar wiwin

Ya kuma bayyana cewa za a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu domin a yanke musu hukuncin da ya dace da su.

Bayan wannan lamarin, hukumar ‘yan sanda ta sake nanata kira ga al’umar Nijar akan bukatar bada hadin kai don ganin an murkushe wannan al’amari da ke ci gaba da biijirowa a kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG