Rahotanni daga kano sun ce jirgin, baya ga kayan yaki da yake dauke dashi, har da wasu kananan jirage masu saukar ungulu guda uku.
Jirgin wanda ba'a bayyana daga inda ya fito ba, an ce yana kan hanyarsa zuwa kasar Cadi, kamin ya yada zango na ba bisa ka'ida ba, domin masu aikin a tashar basu da masaniya gameda zuwan jirgin.
Da yake amsa tambaya ko an san matuka jirgin turawa ne ko bakar fata, Mahmud Ibrahim kwari, yace an killace ma'aikatan jirgin, ba'a basu dama a matsayinsu na 'yan jarida su kai ga inda jirgin ma yake ba.
Zuwa yanzu dai hukumomi basu fito da wani bayani a hukumance dangane da inda wannan jirgi ya fito ba, da kuma inda zai je.
Duk da haka aka ce jirgin yana kan hanyarsa zuwa kasar Cadi ne.
Ga karin bayani.