Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kakabawa Wadansu Tsofaffin Kusoshi Gwamnatin Takunkumi A Sudan Ta Kudu


Salva Kiir
Salva Kiir

Kungiyar Tarayyar Turai ta kakabawa wadansu tsofaffin jami'an Sudan ta Kudu takunkumi jiya jumma'a wadanda aka samu da laifin keta hakin bil'adama da kuma gunguntar da yunkurin wanzar da zaman lafiya.

Takunkumin da dukan membobin Kungiyar Tarayyar Turai zasu aiwatar ya shafi tsohon hafsan hafsoshi Janar Paul Malong, da mataimakin ma'aikatar tsaro janar Malek Reuben Riak, da kuma ministan watsa labarai Michael Makuei Leuth, kuma zai kama aiki ba tare da bata lokaci ba. Takunkumin ya shafi hanasu amfani da kaddarorinsu dake kasashen da kuma haramta masu tafiya kasashen Kungyar Tarayyar Turai.

Ministar Birtaniya kan harkokin Afrika, Harriett Baldwin, tayi na'am da takunkumin ta kuma jadada niyar kasarta ta taimakawa a kawo karshen tashin hankalin a Sudan ta Kudu.

A halin da ake ciki kuma, Hukumomin Sudan ta Kudu sun kori wani limanin Katolika dan kasar Kenya wanda yake aiki a ikilisiyar Yambio Tambura.

Joseph Marko Wanga Bilali, ministan kananan hukumomi da hukumar yan sanda a jihar Tambura ne ya bada umarnin ranar Laraba ga hukumar tsaron kasa da bincike miyagun laifuka CID ta kori Rev. Father Joseph Githinji daga jihar Tambura , wadda ke kan iyaka da jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Wasikar tace ana bukatar Githinji ya fice daga yankin ya kuma kai kansa Yambio ba tare da bata lokaci ba.

Wasikar ta Wanga bata bayyana dalikin tasa keyar limamin dan kasar Kenya ba zuwa kasarsa ta asali.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG