Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Kwamiti Don Tallafawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Imo


Kwamiti da aka kafa don tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Imo
Kwamiti da aka kafa don tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Imo

Gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnatin jihar Imo sun kafa wani kwamiti na musamman, don tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Shugaban sashen gudanarwa na hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA Mista Ifeanyi Nnaji ne ya bayyana hakan, a wata hira da sashen Hausa na Muryar Amurka.

Ya ce, “Hukumar NEMA tana hada gwiwa ne da gwamnatin jihar Imo, kuma mun kafa wani kwamitin da zai duba yanayin, kamar hadarin da na iya tasowa sanadiyyar ambaliyar ruwan. A halin yanzu dai tare da ma’aikatun muhalli, kiwon lafiya, ayyuka, ilmi, da kuma albarkatun ruwa, zamu duba al’amarin mu ga yadda za a taimaka wa wadanda lamarin ya shafa don inganta halin da suka tsinci kansu a ciki.”

AMBALIYA
AMBALIYA

Mista Ifeanyi Nnaji ya kara da cewa hukumar NEMA zata kimanta barna da asarar da aka tabka sakamakon ambaliyar ruwan idan damina ta ragu, don gano adadin gidaje, da hekta na fili, da kuma irin amfanin gonan da lamarin ya salwanta. Ya kuma kara da cewa, gwamnati ta sanya hannu kan samar da kayan tallafi don raba wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.

A nashi bayanin, Yusha’u Imam, Wazirin Hausawan garin Onitsha na jihar Anambra ya yi bayani kan yadda ambaliyar ruwa ta bana ke shafar su mazauna kusa da gabar kogin Neja inda ya ce, “Lallai an samu asarar dukiyoyi da gidaje anan gefen Anambra, ta gefen Anambra East zuwa Ogbaru sosai kuwa, don sakamakon hakan mu kanmu da muke Onitsha bai dai taba gidaje ba. Amma gefen kasuwar Onitshan ta yamma ta nan ruwan yake wucewa, ruwan ya shiga unguwanni da kuma wasu layuka cikin kasuwa, har zuwa inda na’urar kara karfin wutar lantarki ta ke. Yanzu ya kai sati uku bamu da wutar lantarki sakamakon wannan ambaliyar ruwan.”

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

XS
SM
MD
LG