Da yake kaddamar da aikin rigakafin dabbobin a madatsar ruwan Tagwai dake arewa maso gabashin birnin Minna, mataimakin gwamnan jihar Neja Alhaji Ahmed Ketso, yace kyauta ne za’a yi rigakafin dabbobin da suka hada da shanu, tumaki, awaki, karnuka, aladu, har ma da rakuma da kuma maguna.
Domin tabbatar da lafiyar dabbobin, an kuma samar da cibiyoyi a sassan kananan hukumomin jihar da makiyaya zasu kai dabbobin ayi masu rigakafin a cewar mataimakin gwamnan.
Alhaji Isma’ila Rebe, da ya wakilci shugaban Myetti Allah na Najeriya a wajan yace sun yi maraba da aikin rigakafin dabbobin domin wani bangare ne na bunkasa rayuwarsu,
Wani makiyayin mai suna Kiri Baushi kamfanin Bobi, yace duk da yake an dan makara amma aikin rigakafin ya zo akan kari, amma da ace lokacin da dabbobi suka dawo daga mashekari ne da abun ya fi. Sannan ya bukaci a kara yawan maganin rigakafin domin a sami damar yiwa wasu dabbobin dake shigowa daga makwabtan jihohi irin su Kebbi don cin karmami,
Manyan cututtukan da suka fi addabar dabbobin dai sune boro da sammure mai sanya shanu cin kasa idan tayi yawa, sai kuma cutar haukacewar karnuka.
Facebook Forum