An gudanar da bikin ranar a Bauchi da suka hada da yiwa mata lacca da kuma baza kolin naurorin fasahar zamani kala kala.
Hajiya Maryam Maishanu shugaban cibiyar koyawa al'umma yin anfani da naurorin zamani a Bauchi ta yi bayani akan kokarin wayar da kawunan mata dangane da mahimmancin yin anfani da naurorin fasahar zamani.
Tace suna kokarin jawo hankalin mata akan mahimmancin koyo da yin anfani da naurorin zamani domin kusan yin komi yanzu ya ta'allaka ne akan samun ilimin naurorin zamani.
Shi ma Malam Isa Garba jami'in cibiyar nazarin zamani da cigaban al'umma. Yace yin anfani da naurorin zamani zai inganta rayuwar mata. Inda mata zasu mayarda hankali akan naurorin zamani al'umma zata fita daga takunkumin da take ciki, na rashin karfin tattalin arziki. Samun ilimin zai taimaki mata su daina dogara ga abun da maza suka samu kadai. Su yi anfani da naurorin su zama hanyoyin samun kudaden shiga.
Wasu mata da suka halarci taron sun bayyana yadda suke anfani da naurorin zamani. Suna yin karatu. Suna yin bincike cikin yanar gizo. Wata ma tace aikin makaranta baya yiwuwa sai da bincike ta yanar gizo.
Ga karin bayani.