Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An haramta Cin Naman Shanu, Da Wasu Dabbobi Tsawon Wata Guda a Yankin Gabashin Ghana Sakamakon Bullar Cutar Anthrax


Wata daba da anthrax ta kashe
Wata daba da anthrax ta kashe

Majalisar kula da yankin Sama maso gabashin Ghana ta sanya dokar hana yanka, sayarwa da kuma cin naman shanu, tumaki, awaki da karnuka tsawon wata guda sakamakon barkewar cutar anthrax a wasu gundumomi biyu na yankin, lamarin da yanzu haka ya yi sanadin mutuwar mutum daya.

Hakan ya bayyana ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan majalisar yankin Alhaji Abubakari Inusah, a madadin Ministan lafiya Stephen Yakubu, da aka tura wa manema labarai bayan wani taro na kwamitin ba da agajin gaggawa a fannin lafiyar al’ummar yankin da aka yi.

"An samu wasu mutane biyu da suka kamu da cutar a gundumar Binduri, inda daya daga cikinsu ya mutu. Bincike ya nuna cewa, sun ci wata dabba ne mai dauke da cutar anthrax," abin da Ibrahim Fusseini, jami’i a hukumar lafiya ta Ghana reshen gundumar Binduri ya fada wa Muryar Amurka kenan.

Ya kara da cewa, mutane 11 sun kamu da cutar ya zuwa yanzu, sannan dabbobi 4 sun mutu sanadiyyar cutar.

Rigakafin dabbobi
Rigakafin dabbobi

Majalisar ta umurci jami’an kula da dabbobi da su fara allurar riga kafin cutar ta anthrax nan take kuma an umurci masu dabbobi da su fito da dabbobinsu don a yi musu riga kafin cutar.

Wasu al’ummar yankin sun bayyana damuwarsu game da wannan kalubale da ya same su.

Malamin ilmin kimiya a makarantar sakandaren Bawku, ya ce, tun da cutar na kama dabbobi da mutane, suna rokon hukumar lafiya da ta yi kokari ta dakile cutar kafin ta kara yaduwa a cikin mutane da dabbobi.

Malami mai wa’azin addinin Musulunci a Bawku, Shaikh Musa Bagniya, a nasa bangaren ya yi kira ne da a gaggauta magance matsalar, kafin Sallar layya.

Kasuwa sayar da dabbobi ta Apo da ke Abuja, Najeriya
Kasuwa sayar da dabbobi ta Apo da ke Abuja, Najeriya

Namanga Mushiru, dan majalisar gundumar birnin Bawku, ya yi kira ga al’ummar yankin da su bi dokar da hukuma ta gindaya, tare da kai rahoton duk dabbar da ta mutu ga hukumar lafiya. Shi ma ya nanata kiran a yi kokarin magance matsalar kafin Sallar layya.

A nata bangaren ma'aikatar abinci da noma ta kasar, ta ce tana tabbatar wa jama'a cewa tana daukar dukkan matakan da suka dace don dakile cutar.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG