A kowace shekara rikici kan barke a tsakanin makikaya da manoma, lamarin da ke sanadiyyar rayuka da kuma asarar dukiyoyi da dama a dukan bangarorin biyu.
Yayin da yake jawabin bude taron, gwamnan jihar Tawa, Mousa Abdulrahaman, ya bayyana cewa wannan niyya da jama’ar suka dauka abar yabawace kwarai domin idan babu kwanciyar hankali da hadin kai a tsakanin al’umma, babu yadda kasa zata ci gaba.
Alhaji Umarou Wandara, shugaban kwamitin da ya shirya ganawar tsakanin al’ummomin Kwanni, ya ce lallai kwalliya ta biya kudin sabulu domin a cewarsa, yadda jama’a suka nuna goyon baya da halartar tattaunawar ya nuna yadda suka yi na’am da wannan kira.
Hajiya Rabi, ‘Yar majalisar dokoki ta kasa mai wakiltar birnin Kwanni, ta ce suma zasu kawo nasu kokarin domin nuna goyon baya da kuma tallafawa matasa domin sama masu ayyukan yi, da karfafa zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya, ne maudu’in tattaunawar.
Ga cikakken rahoton Haruna Mamman Bako Daga Birnin Kwanni.
Facebook Forum