Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa a Habasha


Wani dan kasar Ethiopia ya na kada kuri'arsa
Wani dan kasar Ethiopia ya na kada kuri'arsa

Al’umar kasar Ethiopia ko kuma Habasha, suna kada kuri’unsu a zaben kasar, wanda ake sa ran zai sake baiwa jam’iyya mai mulki ta EPRDF nasarar yin wani wa’adin shekaru biyar.

Rahotanni sun ce komai na gudana kamar yadda aka tsara a Addis Ababa, babban birnin kasar, inda aka samu dogayen layukan masu kada kuri’a.

Jam’iyyun adawa sun yi ikrarin cewa zaben ba shi da sahihanci domin hukumomin kasar suna kama ‘yan adawa da masu shafukan internet da kuma ‘yan jarida.

Koda yake jam’iyyar ta EPRDF ta musanta wadannan zargin.

A zaben shekarar 2010, jam’iyyar ta lashe kusan dukkanin kujerun ‘yan majalisu, wanda zabe ne da aka gudanar cikin lumana, ba kamar wanda aka yi a shekarar 2005 ba, wanda ya haifar da mummunan rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 200.

Akalla mutane miliyan 37 ne ake sa ran za su kada kuri’unsu a wannan zabe, ana kuma sa ran samun sakamakon zabe nan da tsakanin kwanaki biyu zuwa biyar.

Wakilan kungiyar tarayyar Afrika su 59, sun kasance sune kadai masu sa-ido a wannan zabe, domin ba a gayyaci cibiyar nan ta Carter Centre da ke Amurka da kuma kungiyar tarayya turai ba, kamar yadda aka yi a zabukan da suka gabata.

Wadannan zabuka, sun kasance sune na farko, tun bayan mutuwar tsohon Firai ministan kasar Meles Zenawi a shekarar 2012.

Ana sa ran Firai minister mai ci a yanzu, Haliemariam Desalegn zai ci gaba da kasancewa akan karagar mulki bayan zaben.

Shugaba Donald Trump ya ba gwamnatinsa damar tasa keyar bakin haure daga kasar, da kai wasu kurkuku na Guantanamo Bay dake Cuba
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Shehu Kanam mai sharhi kan al’amura ya mana karin bayanin matsayin dalilan yawaitar fashewar tankokin man fetur a Najeriya
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Karin haske akan dalilan dake kawo aukuwar haduran tankar mai a Najeriya da musabbabin karuwar wannan lamari a baya-bayan nan
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG