Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Habaka Harshen Hausa Na Hadin Gwiwar Najeriya Da Burkino Faso


Lokacin gudanar da taron habbaka harshen Hausa a Burkina Faso
Lokacin gudanar da taron habbaka harshen Hausa a Burkina Faso

A wani kokarin neman habaka harshen Hausa a ciki da wajen kasar Burkina Faso, hukumar nazarin harshen Hausa ta kasar tare da hadin gwiwar Jami’ar gwamnatin tarayyar Najeriya ta Dutsen Ma da ke jihar Katsina sun shirya wani taron horar da malaman harshen Hausa a birnin Ouagadougou.

OUAGADOUGOU, BURKINO FASO - Taron ya sami halartan jama'a da dama ciki har da masana ta fannin koyar da harshen Hausa da mataimakin sakataren hukumar kula da harsuna ta kasar Burkina Faso da dai sauransu.

Yayin da yake jawabi a taron, shugaban hukumar Hausa ta kasar Mallam Abdu Rahman Na Garba ya ce horar da malaman harshen da suka yi shi ne matakin farko na neman karfafa harshen Hausa tun bayan da gwamnatin kasar Burkina Faso ta bukaci hukumomin harsuna daban-daban na kasar su fara gudanar da ayuka domin raya harsunansu ta yadda za'a rika koyar da su a makaratun kasar.

Wasu sun samu takardun shaidar koyar da Hausa a taron da aka gudanar na habbaka harshen Hausa a Burkino Faso
Wasu sun samu takardun shaidar koyar da Hausa a taron da aka gudanar na habbaka harshen Hausa a Burkino Faso

Ya ce "dalilin da ya sa muka shirya wannan taro shi ne mu baiwa malamai masaniya ta yadda za su samu su koyar da daidaitacciyar Hausa bisa ka’ida da kuma dokar kasar ta Burkina Faso."

Ya kara da cewa "Mutum ashirin ne muka baiwa wannan horon, cikinsu akwai mata shida maza goma sha hudu. Ita ma'aikatar ministan ilimi da yaki da jahilci da habbaka harsunan kasar Burkina Faso ta ba da takardun shaida da aka baiwa daliban tare da shi babban Malamin wato Farfesa Bashiru Aliyu Sallau. A duk inda mutum ya je da wannan takardar zai iya ya koyar da harshen Hausa, don haka muna farin ciki"

Farfesa Bashiru Aliyu Sallau mai koyarwa a sashen Hausa na jami’ar tarayyar Najeriya ta Dutsen Ma da ke jihar Katsina, shi ne wanda ya horar da malaman harshen Hausa da adadinsu ya kai ashirin, kuma sun koyi fannonin nazarin Hausa guda uku da suka hada da bangaren harshe tare da ala'adun bahaushe da sauransu.

Taron habbaka harshen Hausa a Burkino Faso
Taron habbaka harshen Hausa a Burkino Faso

Farfesan ya kuma kara da cewa sun gana da manyan jami’ar Burkina Faso da ke Oaugadougou kuma abin da suka cimma a yanzu shi ne samar da sashen koyar da harshen Hausa a jami’ar ta yadda dalibai a kasashen renon Faransa da ke Afrika ta Yamma za su dinga zuwa kasar ta Burkina Faso domin neman ilimin harshen.

Hukumomi a Burkina Faso na kokarin tabbatar da samar da wasu harsuna da za'a dinga koyarwa a makarnatun kasar tun bayan da gwamnatin kasar ta bukaci ficewar Faransa.

-Hamza Adam

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG