Matasan dai wadanda suka ce sun damu matuka akan wannan matsala sun je jihar Kwara ne saboda lura da yadda jami'an tsaron kungiyar Amotekun suka fara koro miyagun suna shigowa jihar Kwara.
Al'amarin da ke bukatar daukar matakin gaggawa a cewar shugaban kungiyar matasan yankin Arewa, Muhammed Abdullahi Muhammed.
"Ko shekaranjiya sai da aka harbe wani soja wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Kwara, a yanzu dai muna kokarin kai wa manya koke ne domin a magance matsalolin nan."
Jihar Neja na daya daga cikin wuraren da matsalar tsaro ta mammaye ita ma. Tsohon shugaban karamar hukumar Shiroro ASP Yarima Abdullahi ya sheda wa Muryar Amurka cewa tura ta kai bango domin kusan kullun sai 'yan bindiga sun kai masu hari.
"Ko wacce rana sai an kai muna hari, kuma an kwashe mana shanaye an kuma hana mu shukar doya."
Shima dai Sarkin Hausawan ma'undu da ke yankin karamar hukumar Mariga a jihar Nejan wanda ke gudun hijira a yanzu haka ya ce ya sha da kyar bayan da 'yan bindigar suka hallaka masu mutane da dama.
"Sun taba dauka ta a kwanakin baya, kuma kullun cikin barna suke yi mana."
Ita dai rundunar 'yan sandan jihar Nejan ta ce ta na kokarin fatattakar 'yan bindigar ta hanyar kara tura jami'an tsaro a yankunan kananan hukumomin da lamarin yayi kamari.
Facebook Forum