Yau babban hafsan sojojin Najeriya Manjo Janar Yakubu Tukur Burutai ya mikawa Manjo Janar Iliyasu Isa Abba takardar zama kwamandan rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa da zata yaki Boko Haram.
An yi wannan bikin ne a hedkwatar sojojin Najeriya dake Abuja. Janar Abba shi ya maye gurbin Janar Burutai wanda yanzu shi ne hafsan sojojin Najeriya.
Janar Burutai yace barazanar tsaro a yankin tafkin Chadi ya sa kasashen yankin tafkin suka kafa rundunar wadda hedkwarta na birnin N'Djemina babban birnin Chadi.
Tuni aka girke dakarun soji a N'Djemina da kuma zayyana mata yadda zata tunkari ta'adancin da kungiyar Boko Haram ke haddasawa a kasashen yankin.
Rundunar zata kama aikin gadan gadan.
Rundunar tana samun tallafi daga Majalisar Dinkin Duniya da tarayyar Turai da kuma tarayyar Afirka ko AU da ma sauran kungiyoyin kasa da kasa.
Janar Burutai yace tuni har tarayyar Afirka a madadin rundunar ta karbi tallafi daga tarayyar Turai da kuma kasar Birtaniya domin tabbatar da samun nasarar fafatawar da zasu yi da Boko Haram.
Tuni Najeriya ta bada tallafin dalar Amurka miliyan 21.
Aikin rundunar shi ne fatattakar 'yan Boko Haram da karya lagwansu da kuma kawo karshensu gaba daya kana a ceto 'yan matan Chibok.
Rundunar zata yi aikin jinkai ta kuma tabbatar garuruwan da aka kubutosu daga kungiyar Boko Haram basu sake komawa hannunta ba.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.