Wata 'yar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar kaltungo da kuma shongom, Hajiya Binta Bello, ta mikawa gwamnatin jahar Gombe, makullan cibiyar bincike kan cizon majizai, da kuma samar da magungunan da zasu warkar da su.Ta gina cibiyar ce a kauyen Tula, mai tsaunuka
Da take jawabi a bukin, Hajiya Binta tace ta dauki wannan matakin ne domin saukakawa mazauna yankinta da kuma ma yankin arewa maso gabashin kasa, hara kamaru matsalar neman magunguna. Domin cibiyar zata kawar da wannan matsala, saboda zata samar da su kuma cikin sauki, maimakon yanzu inda allura daya yake kaiwa sama da Naira dubu talatin.
A jawabin karbar makullan cibiyar, kwamishinan kiwon lafiya na jahar Gombe Dr. Ishaya Kennedy, wanda ya wakilci Gwamnan jahar, ya bayyana farin cikinsa ga samun wannan cibiya. Yace cibiyar sara ce kan gaba,domin duka duka mako daya ne da kammala taron da masana kiwon lafiya daga kasashen Afirka da aka yi a Legas, domin karfafawa da kuma inganta hanyoyin sarrafa magunguna a cikin gida.
Sarkin Kaltungo Injiniya Sale Mohammed, ya jinjinawa 'yar majalisar domin cizon majiji shine daya daga cikin matsaloli da suka fi addabar yankinsa.
Facebook Forum