Hoton wani kifi da aka yi ittifakin cewar ya yi kama da fuskar mutun na neman fasa yanar gizo, wasu kafafen sadarwar intanet da dama su ka kafe wannan bidiyon, wanda ya nuna kifin yana kama da mutun, ya na da surar fuskar mutun, hanci ido da baki duk a waje daya ba kamar yadda akan san kifi ba.
A cewar wani wanda ya rubuta nashi ra’ayin dangane da bidiyon kifin, “ai wannan kifin na da kyau fiye ma da mutane,” sai wani shi ma ya ce “ai kuwa wannan kifin ya fi ni kyau.” Shi kuwa wani cewa ya yi “anya kuwa wannan ba wani ne wanda ya ci amanar matar shi, ta je wajen boka ya maida shi haka ba?”
Shi kuwa wani cewa yayi kila fa China ce ta kirkiri wannan kifin don ta shiga cikin duniya, har ya zuwa yanzu ba a tantance asalin wannan bidiyon dake yawo na kifin ba.
Facebook Forum