Wani sabon bincike na kasa da kasa da aka yi, ya nuna cewa yiwa wadanda suka kamu da cutar kanjamau jinya nan da nan maimakon bari sai cutar tayi tsanani yana rage barazanar su ta harban wasu da kwayar cutar nesa ba kusa ba. Sakamakon farko da aka gabatar a ranar Alhamis ya nuna cewa mutanen da aka yiwa jinya nan da nan ba zasu yada kwayar cutar ba da minzanin wajen kashi casa'in da shidda daga cikin dari. A cikin mutane mata da miji dari takwas da saba'in da bakwai wadanda suka kamu da kanjamau amma basu fara jinya nan da nan ba, mata da miji ashirin da bakwai ne suka harbu da kwayar cutar kanjamau. To amma daga cikin wadanda suka fara jinya nan da nan mata da miji daya ne kawai suka harbu da kwayar cutar. An shirya kamalla wannan gwaji ne a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, to amma an gabatar da sakamakon binciken da wuri ne a saboda anga abun ba zata. Shugabar kungiyar Lafiya ta duniya Margaret Chan ta baiyana sakamakon binciken a zaman abinda zai dora tasiri ga shirye shiryen rigakafi nan gaba.
Wani sabon bincike kasa da kasa da aka yi ya nuna cewa yiwa wadanda suka harbu da kwayar cuyar kanjamau, nna rae barazanarsu ta yada cutar. Jiya alhamis aka gabatar da sakamakon wannan bincike.