‘Yan Rwanda sun kada kuri’ar zaben shugaban kasa a karo na biyu tun bayan kashe-kashen kare-dangi na 1994, kuma ana sa ran shugaba mai ci Paul Kagame zai lashe wannan zabe da gagarumin rinjaye.
Masu jefa kuri’a da yawan gaske sun fito suka fara layi tun kafin fitowar rana a yau litinin. Jami’an zabe suka ce da alamun komai ya tafi sumul a duk fadin rana a yau din.
A yanzu dai an fara kidaya kuri’u, kuma ana sa ran samun sakamakon zaben nan gaba yau litinin ko kuma gobe talata.
Shugaba Kagame yayi takara da wasu mutanen uku, wadanda duk su na da alaka da jam’iyyarsa ta "Rwanda Patriotic Front" mai mulkin kasar.
Masu hamayya da shugaba Kagame sun bayyana yakin neman zaben da aka yi a zaman na bogi. Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce an hana jam’iyyun hamayya na zahiri tsayar da ‘yan takara a wannan zabe.
A lokacin da yake kada kuri’arsa a yau litinin, Mr. Kagame yayi watsi da sukar da ake yi wa gwamnatinsa. Ya bayyana zaben a zaman na dimokuradiyya sosai, ya kuma ce shi bai ga wata matsala ba.