Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Dokar Hana Fita A Sokoto


Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Sokoto ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da hannu a kisan Samuel wacce ‘yar asalin jihar Neja ce da ke karatu a kwalejin ta Shehu Shagari.

Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta dage dokar hana fita da aka saka a birnin, sakamakon zanga-zanga da mutane suka yi don a sako wasu matasa biyu da ake zargi da hannu a kisan wata daliba da ake zargi da yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

A ranar Alhamis din makon jiya, aka zargi Deborah Samuel, daliba a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke birnin Sokoto da yin batanci ga fiyayyen halitta, lamarin da ya sa dalibai suka kashe ta.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Sokoto ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da hannu a kisan Samuel wacce ‘yar asalin jihar Neja da ke karatu a kwalejin ta Shehu Shagari.

Sai dai kama matasan ya janyo zanga-zangar neman a sake su a ranar Asabar a birnin na Sokoto, lamarin da ya sa gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya saka dokar hana fita ta sa’a 24.

Amma a wata sanarwa da Kwamishinan yada labaran jihar Isah Bajini Galadanci ya fitar a ranar Juma’a, gwamnati ta ce ta dage dokar baki daya.

“Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Mutawallen Sokoto, ya dage dokar hana fita da aka saka a Sokoto da kewaye kamar yadda dokar kasa ta ba shi ikon yi, bayan tuntuba da aka yi.” Sanarwar ta ce.

Sanarwar ta kara da kira ga jama’ar jihar da su kasance masu bin doka da oda a ko da yaushe, tana mai nuni da muhimmancin zaman lafiya a tsakanin jama’a.

“Sai dai gwamnati ta hana duk wani tattaki a jihar har sai yadda hali ya yi.”

XS
SM
MD
LG