Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci Gaba DA Yaki Da Ebola


The White House
The White House

A karshen watan Maris, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya sanar da cewa, gwamnatin Amurka ta ware kudi har dala miliyan 30 don hanzarta bada tallafi ga barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Jamhuriyar Guinea.

Tallafin zai kuma taimaka wajen karfafa shirye-shiryen cutar ta Ebola a cikin kasashen kan iyakar masu hatsarin gaske na Cote D'Ivoire, Liberia, Mali, Rwanda, Senegal, Saliyo, da Uganda.

Cutar Ebola zazzaɓi ne mai tsanani wanda aka fara gano ta a shekarar 1976 a cikin ƙasar da yanzu aka fi sani a matsayin Jamhuriyar Demokiradiyyar Congo, kusa da kogin Ebola.

Tsakanin 1976 da 2012, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, an gano barkewar cutar 24 a yankin Afirka da ke Sahara, wanda ya haifar da kusan mutane 2,400 da suka harbu tare da mutuwar 1,590.

Bayan haka ne aka samu barkewar cutar mafi girma, wacce ta faru a Yammacin Afirka tsakanin Disamba 2013 da Janairu 2016: Mutane 28,646suka harbu kuma 11,323 suka mutu. Kananan ɓarkewar cutar ta biyo baya a cikin 2017 da 2018. Wata babbar barkewa ta biyu ya faru a gabashin DRC daga 2018 zuwa 2020. Wannan ita ce ɓarkewar cutar ta Ebolamafi girma ta biyu a tarihin duniya, kuma mafi muni a tarihin DRC, kuma na farko a cikin yanki mai cike da rikici.

Cutar tana yaduwa ne ta hanyar mu'amala da ruwan jikin dabbobi ko mutane masu cutar. Kamuwa da cuta na iya faruwa daga taɓa jikin waɗanda suka mutu daga cutar ta Ebola yayin ayyukan binne waɗanda suka haɗa da taɓa jiki ko kuma wanke jikin.

Kungiyar Lafiya ta Duniya, ko WHO, ta ba da rahoton cewa kulawar ba da tallafi da wuri da kuma haɗin gwiwar jama'a su ne mabuɗin ceton rayuka da kuma shawo kan ɓarkewar cuta. Don hana manyan ɓarkewar cutar ta Ebola, ana buƙatar sa ido kan cututtuka don ganowa da amsawa cikin hanzari da tasiri ga sabbin harbuwa a ciki da kewayen wuraren da abin ya shafa.

Tallafin da ya kai dalar Amurka miliyan 30 daga gwamnatin Amurka zai taimaka wajen bin diddigin masu hulda, da kuma dakin gwaje-gwaje da ma gwajin cuta. Hakan zai kai ga kafa cibiyar kula da cutar ta Ebola da cibiyoyi, da kuma karfafa rigakafin kamuwa da cutar a manyan cibiyoyin kiwon lafiya.

Cututtuka masu saurin yaduwa kamar Ebola ba sa mutunta iyakokin ƙasa kuma suna iya yaduwa cikin hanzari, da yin illa ga lafiya, tsaro, da ci gaban kowace ƙasa. Gwamnatin kasar Amurka na alfaharin bayar da gudummawa ga yunƙurin magance wannan mummunar cuta da kuma lafiyar duniya baki ɗaya.

XS
SM
MD
LG