Nijar-Hukumomi a yankin Agadez sun ce sun ceto bakin haure 24 a wani wuri mai tazarar kilomita 50 daga hamadar da ake kira Sageden.
Ana kyautata zaton cewa ‘yan gudun hijirar, suna kan hanyar zuwa Libya ne ko Aljeriya, da zummar ketarawa zuwa Turai.
Hukumomin suka ce mutane 15 ne aka tabbatar da mutuwar su. Amma wasu rahotanni daba’a tabbatar da su ba suna cewa, bakin haure 50 ne suka halaka. Bayan da masu safarar su suka kayle su a cikin motoci uku dauke da mutane 75. Suka bar su a cikin hamada babu abinci da ruwa.
Musa Changari, wanda jami’i ne na kungiyar farar hula dake tallfawa ‘yan gudun hijira da bakin haure, yace masu safarar mutanen, suna ta kirkiro da sabbin hanyoyi ne cikin hamada, bayan da hukumomi suka dauki matakai na sa ido kan hanyoyin da suka saba bi.
Wani matashi Hinse Garba, yayi kira ga matasa na Afrika su jajirce su nemi rayuwa a kasashen su, maimakon jefa rayukan su dana iyalansu cikin hadari na neman zuwa turai.
Musa Changari, yayi kira ga hukumomin kasashen da suke Afirka, su kuma su maida hankali wajen inganta rayuwar matasa, muddin anan son ganin karshen kwararar matasa tare da yara kanana da mata, wadanda suke kokarin zuwa turai domin neman inganta rayuwar su a wata kasar.
Facebook Forum