Hakan dai na daga cikin matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka wajen nemo sauran fursunonin da suka tsare daga gidan gyara hali na kuje a makon jiya.
Gwamnatin kasar dai ta ci alwashin kamo sauran wadannan bata gari da tuni kungiyar mayakan ISWAP ta dauki alhakin kai harin da kuma kubutar da su.
Wannanan lamarin ya haifar da cunkoso sosai na ababen hawa sakamokon jibge sojoji a kan tituna wadanda suka sanya shingaye akan hanya da nufin neman 'yan ta'adda da suka tsere, musaman ma dai a titunan da suka hada birnin da wasu jihohi da ke da makwabtaka, da ya kai ga nasarar kama wasu daga cikin fursunonin da suka yi kokarin harcewa.
Rahotanin dai sun yi nuni da cewa jami’an 'yan sanda sun kama daya daga cikin fursunonin na kuje a karamar hukumar keffi ta jihar Nassarawa, kazalika hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya wato NDLEA ta sanar da cewa ta yi nasarar kama guda daga cikin fursunonin a anguwar Area 1 dake cikin birinin na Abuja, yayin da a jihar Ogun yan’sanda suka bayyana cewa an kama wani da ya tsere daga gidan yarin na Kuje a yankin Sango-Ota da ke jihar.
Wannan kokari dai na nuni da cewa jam’an tsaro a Najeriya ba su ga ta zama ba har sai bukata ta biya na nemo sauran mugun irin da ke cikin al’umma.
Saurari rahoton Shamsiya Hamza Ibrahim cikin sauti: