An fara gudanar da wasan nan na wasa kwakwala da ake kira "Computer Games" a Najeriya.
Gasar ta bana, wadda aka fara a birnin Lagos, ta samu halartar matasa sama da 500, wadanda za su yi taron karawa juna sani cikin kwana biyu.
Sannan za a kwashe kwana biyu ana baje kolin basirar kowane matashi., baya ga haka, masana daga kamfanin Epic za su horar da masu halartar taron.
A gasar wannan shekarar, ta matasa masu hazakar rubutun wasan kwamfuta game, wanda aka fara yau zuwa ranar 8 ga wannan watan, wanda wasu kungiyoyin kasashen Afirka da na cikin gida a Najeriya suke gabatarwa a kowace shekara.
Za’a ilmantar da su hanyoyin inganta tsare-tsare da suke da su na shirya wasan kwamfuta game, da kuma yadda za’a yi amfani da shirin wajen aiwatar da wasu ayyukan da suka shafi sauyin zamani.
Daga karshe za’a zabi matasa biyu da suka gabatar da game wanda ya fi kowannen.
Za’a ba su kyaututtuka kana a hada su da wasu kamfanonin kasashen turai don su ba su horo na musamman wajen shirya wasan kwamfuta game da za’a iya amfani da shi a duk fadin duniya.
Facebook Forum