Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana cewa an shiga bala’in yunwa a wasu yankuna biyu na kudancin Somaliya a yayin da yankin kuryar arewa maso gabashin Afirka yake fama da karancin ruwan sama mafi muni cikin shekaru masu yawan gaske.
Yau laraba majalisar ta ce ana fama da bala’in yunwa a yankunan Bakool da Shabelle ta Kasa, kuma babban sakataren majalisar, Ban Ki-moon, yayi gargadin cewa wannan bala’i zai yadu idan har ba a dauki matakan gaggawa na magance matsanancin karancin abincin da ake fama da shi ba.
Mr. Ban ya fadawa ‘yan jarida a New York cewa ‘yan Somaliya su na mutuwa da yawan da ya wuce kima, kuma duk wani jinkirin da aka samu yana kara yawan hasarar rayukan ne kawai.
Babban jami’in ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Somaliya, Mark Bowden, yace Somaliyawa miliyan 3 da dubu 700 ne, watau kusan rabin mutanen kasar, suka shiga cikin ukuba, inda dubbai suka mutu saboda rashin abinci.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kasar Somaliya kawai, ana bukatar agaji na dala miliyan 300 a cikin watanni biyun dake tafe. Yau laraba, Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta dora sha’anin takalar bala’in karancin abinci a gabashin Afirka ya kai mizanin mafi muhimmanci a duniya. Ta ce ana bukatar kaddamar da gagarumin aikin agaji domin kaucewa mace-mace, ganin cewa akwai mutane miliyan 11 a yankin dake bukatar agajin abinci.