Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa A Janhuriyar Nijar Sun Yi Gangamin Kashedi Kan Shirin Magudin Zabe


Shugaba Mohammadou Issoufou na Janhuriyar Nijar
Shugaba Mohammadou Issoufou na Janhuriyar Nijar

Yayin da siyasar Janhuriyar Nijar ke cigaba da zafi, 'yan adawa sun yi gangamin nuna rashin amincewarsu da abin da su ka kira shirin yin magudi

A Jamhuriyar Nijar, jam’iyyun kawancen hamayya sun gudanar da jerin

gwano hade da taron gangami a yau lahdi a birnin Yamai domin

kalubalantar gwamnatin Mahammadu Isuhu da suke zargi da niyyar

tafka magudi a zabubukan da za a yi badi a Nijar.

Wakilin Muryar Amurka Sule Mumuni Barma ya aiko mana da wannan rahoton.

Zargin gwamnatin Jamhuriya ta bakwai da kokarin shirya magudi a

zabubukan badi hade da nuna kin yarda da sahihancin kotun tasrin

mulkin kasa, sune manyan batutuwan da suka kai kawancen ‘yan

hamayya fitowa titunan Yamai domin jan hankalin mahukuntan kasar

Nijar su canza tunani kamar yadda Madame Bayer Maryama

Gamatche ke fada a gaban dubban magoya bayan FPR da suka yi jerin

gwano daga dandalin Place Toumo zuwa dandalin Place de la

Concertation.

To sai dai a nasu bangare, shugabannin jam’iyar PNDS TARAYYA mai mulki,

a ta bakin Alhaji Asumana Mahammadu, sun musanta wannan zargi.

Wannan shine karon farko da ‘yan adawa ke fitowa kan tituna, tun

bayan zanga zangar da suka gudanar a farkon wannan shekara ta 2015

inda aka yi ba ta kashi tsakaninsu da jami’an tsaro saboda dalilan da

hukumomin Yamai suka kira na rashin bayar da izini.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG