Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka za ta taimaka ma Ghana Wajen Zamanantar da Bangaren Shari’arta


Shugaban Ghana Nana Akufo
Shugaban Ghana Nana Akufo

Amurka ta bayyana aniyarta ta taimaka ma kasar Ghana wajen garanbawul da kuma zamantar da bangaren shari’arta saboda a rika tabbatar da adalci. Wannan na kunshe cikin sakon da Ofishin Jakadancin Amurka a birnin Accra na kasar Ghana ya tura ta kafar tuwita biyo bayan wata ganawa tsakanin Jakadiyar Amurka a Ghana Virginia Palmer da Alkalin Alkalan Ghana, Anin Yeboah.

Tuni masu ruwa da tsaki su ka fara tsokaci kan wannan tayi na Amurka. Dr. Irbard Ibrahim ya ce lallai akwai bukatar zamanantar da bangaren na shari’a, amma ba kawai a Ghana ba, har ma da Amurkar kanta. Ya ce da alamar akwai banbanci wajen yadda ake yanke hukunci ma fararen fata da bakaken fata a Amurka. Fararen fata, in ji shi, su kan samu rangwame idan aka kwatanta da irin hukuncin da ake yanke ma bakaken fata.

Dr Ibrahim ya kara da cewa, rashin daukar matakin kwarai kan wasu jinsuna idan sun aikata laifuka ko rashin adalci ma wadanda aka yi wa laifi, na sa irin wadannan jinsuna su kullaci hukuma ko ma al’umma baki daya.

Ya ce kasar Ghana na fama da wannan nau'i na rashin adalci a bangaren shari'arta. Don haka, a cewarsa, akwai bukatar yin garanbawul.

Cikin wadanda ke maraba lale da wannan tayi da Amurka ta yi na bayar da gudunmawa wajen inganta tsarin shari’ar Ghana, akwai Malam Issah Mairago, wani mai fashin baki.

Saurari cikakken rahoton Ridwan Mukhtar Abbas:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG