Ofishin jakadancn Amurka a Najeriya ya jaddada anniyarsa na hadin gwuiwa da Najeriya wajen inganta harkokin talibijan domin fahimtar al'adun juna da hanyar cudanya tsakanin Amurka da Najeriya.
Jami'in sashen al'adu na ofishin jakadancin dake Abuja Larry Socha, wanda ya jagoranci tawagar Amurkawan zuwa Jos, ya ce sun zo da wata kwararriya a ayyukan talibijan Angelina Burnett, daga birnin Los Angeles a nan Amurka domin ta taimakawa masu aiki finafinai da dabaru domin ingata aikinsu.
A jawabinsa Mr. Socha, ya ce manufar hadakar ita ce yadda ake hada finafinai a kasar Amurka da yadda za'a bada labari mai inganci cikin dan karamin lokaci.
Ita ma Angeina Burnett, ta ce ta zo Najeriya ne domin ta taimakawa masu harkokin talibijan da bayanai kan yadda zasu gudanar da ayyukansu su jawo hankalin masu kallonsu su ilimantar dasu cikin nishadi da annashuwa.
Ta ce akwai koyaswa akan al'adu, tattalin arziki, zamantakewa, da yin adalci da yakamata masu hada fina finai su bada fifiko akansu domin bayyana irin dabi'un da zasu kawo hadin kai da zaman lafiya.
Shugabar cibiyar koyon dabarun hada finafinai ta kasa dake Jos Christiana Best ta ce baututwan da Angelina ta yi zasu taimaka kwarai.
A saurari rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum