Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Zargi Shugabannin Sudan ta Kudu da Jefa Kasar cikin Yaki


'Yan gudun hijiran Sudan ta Kudu sanadiyar yakin basasa
'Yan gudun hijiran Sudan ta Kudu sanadiyar yakin basasa

Jami’an Amurka dake bada shawarwari akan harkokin tsaro ta soki kasar Sudan ta Kudu da babban murka saboda bukukuwan samun ‘yancin kai da take yi a halin yanzu, tana mai cewa Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa kuma shugaban ‘yan tawaye Riek Machar sune musabbabin yakin da ya dai-daita kasar kuma ake cigaba da yi a kasar.

Susan Rice, tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta fada a wata sanarwa da ta fitar yau Alhamis cewa duk da farin cikin da Sudan ta Kudu take yi na samun ‘yancin kai a shekara ta 2011, lamarin wannan kasa na sosa mata rai matuka.

Ta ce a watanni 19 da suka gabata, gwamnatin Sudan ta Kudu ta kauracewa ayyukan da suka rataya a wuyanta, inda ta gagara tsaron rayuka da kadarorin ‘ya’yanta, kuma tayi fatali da ingancinta, yayinda tashe-tashen hankula suke cigaba tare da rigingimun siyasa.

XS
SM
MD
LG