Matasan da suka shahara a sha'anin jagoranci su ne zasu wakilci kasar Nijar a shirin YALI na wannan shekarar a kasar Amurka.
Zasu shiga ayarin matasa daga kasashen Africa da na Amurka a shirin YALI. Shi dai shirin YALI taron karawa juna sani ne tsakanin matasan kasashen Afirka da Amurka.
Mawakiya Safiya Amin Lamin na cikin wadanda suka riga suka karbi tikitin zuwa Amurka daga ofishin jakadancin Amurka dake Nijar domin shirin YALI na shekarar 2017.
Safiya tace duk wanda ya sami sa'ar zuwa shirin ya dage yayi aiki domin tafiya ce ta zuwa yin koyon hanyoyin da zasu kara masu kwarewar yin ayyukansu da kyau. Safiya zata tafi Staten Island ne a cikin jihar New York. Zata kara koyon ayyukan shugabancin jama'a.
Jakadiyar Amurka a Nijar ta yiwa matasan nasiha inda ta gargadesu da su yi muamala da sabbin abokai saboda duk wani Ba'amariken da zasu gamu dashi a tafiyar tasu zai so ya kulla hulda dasu kuma zai ji dadin sanin kasarsu sosai. YALI wani shiri ne kuma na haduwa ce ta musayar al'adu tsakanin Amurka da sauran kasashen duniya.
Malam Mamman Usman daya daga cikin wadanda suka taba zuwa taron YALI a shekarar 2015 ya jawo hankalin tawagar ta bana cewa YALI ba wasa ba ne. Mutum zai tashi karfe shida na safe har zuwa takwas na yamma yana cikin aji. Yace su maida hankali su yi koyo.
Ranar 14 ga wannan watan matasan zasu tashi zuwa nan Amurka kuma zasu yi makonni shida suna daukan karatu tare da ziyarar wurare daban daban. Shugaba Barack Obama ne ya kirkiro shirin YALI.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum