Mai Magana da yawun Fadar White House Ned Price yace wannan ba karamin ci gaba ba ne ga kasar,wadda ta fito daga cikin yakin basasa a shekarar 2003 kuma ta tsaya tsayin daka domin ganin ta karfafa demokaradiyya da harkokin tattalin arziki a cikin kasar.
Price Yace kasar bata tsaya a ganin ta taka rawar gani a harkokin kafuwar demokaradiyya ba kawai, harma da yaki da cutar Ebola wadda ta nemi kawo wa kasar cikas a dai-dai lokacin da take kokarin habbaka harkokin demokaradiyyar ta, da bunkasa tattalin arzikin ta, da samar da ababen more rayuwa ga yan kasa, tare da inganta matakan tsaro.
Sai dai Fadar ta White tace har yanzu da sauran rina a kaba a kasar domin ko akwai batun ganin Majalisar Dinkin Duniya ta tsame hannun ta daga harkokin tsaron kasar tare da ganin an samar da zaben shugaban kasa a shakarar 2017.
Sai dai Price yace ba shakka yan kasar ta Liberia a shirye suke su rungumi wannan babban kalubale.