Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Tallafawa Nigeria A Fannin Noma


 Stuart Symington, Jakadan Amurka a Nigeria
Stuart Symington, Jakadan Amurka a Nigeria

Kokarin da kungiyar raya kasashe masu tasowa ta gwamnatin Amurka da ake cewa USAID keyi na tallafawa Nigeria zama mai dogaro da kai ta fuskar abinci, kungiyar USAID ta shirya taron bita ga wasu malaman bangaren noma na jami’oin Nigeria

A wani jawabi data gabatar daga jami’ar Michigan na kasar Amurka ga mahalarta taron, babban jami’a dake lura da shirin hadin guiwan na kasar Amurka Dr Saweda Liverpool Tasie, tace shirin na daya daga cikin tallafin da Amurka ke bayarwa ga kasashen waje da kuma shirin gwamnatin Nigeria na maida kasar mai dogaro da kai ta fuskar abinci .

Bugu da kari Jami’ar Michigan da ta yi suna wajen koyar da aikin gona a Amurkan ta bada gurabe ga dalibai dake nazarin fannin noma na zuwa Amurka domin samun horo na zangon karatu rabin shekara ga masu karatun digiri na biyu da kuma shekara guda ga masu karatun digirin digirgir wato dakta.

Dakta Baba Abdullahi malamin sashen aikin noma ne daga jami’ar Ahmadu Bello Zaria…yace samar da abinci shine kashin bayan arzikin kowace kasa, kuma matakin gwamnatin Amurka na tallafawa Nigeria abin yabawa ne matuka, wanda ya zama abin koyi ga sauran kasashe. Yace dole ne a samu horoswa na zamani kafin kudirin gwamnati ya samu nasara a wannan fanni.

Wasu daga cikin dalibai kuma malaman nazarin aikin noma da zasu ziyarci Amurka domin samun horon dai sun hada da Malama Fatima Sule daga Jami’ar IBB dake jihar Niger, wadda itace daliba guda mai karatun digirin digirgir kacal daga arewacin Nigeria, ta yaba da matakin gwamnatin Amurkan da Nigeria na tallafawa harkar noma domin dogaro da kai, tare da karatu tukuru domin baiwa mara da kunya a lokacin karatun nasu.…..

Batun samar da wadataccen abinci dai ya kasance daya daga cikin kudirorin gwamnatin Nigeria, na maida kasar mai dogaro da kai ta fuskar abinci.

A saurari rahoton Babangida Jibrin

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG