Rundunar sojin Amurka na duba wasu hotunan da aka dora a dandalin sada zumunta na Twitter wadanda suka nuna sojojinta da aka kashe a Jamhuriyar Nijar a shekarar da ta gabata.
A jiya Laraba,rundunar sojin Amurka da ke yankin Afirka ta AFRICOM, ta ce tana sane da hotunan da aka dora a shafin na Twitter.
ta kuma ce tana kan nazarinsu domin ta tantance gaskiyar lamarin na cewa ko akwai wani faifan bidiyo mai alaka da sojojin da aka kashe.
Bayanan da aka wallafa sun nuna cewa an samo hotunan ne daga wani bidiyo wanda ke da tsahon fiye da minti 10 wanda wani mai hadin gwiwa dan kungiyar IS a Mali ya fitar.
Ya kuma kara da cewa bidiyon ya nuna wani sojan Amurka da rauni ajikinsa tare da gawarwakin sojojin Amurka uku da aka kashe a watan Oktoban da ya gabata.
Harin ta'addancin da aka kai a kusa da kauyen Tongo Tongo ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Amurka 4, sojojin Nijarr 4 da kuma tapinta dan Nijar guda.
Ana sa ran za'a kammala binciken da ake yi akan lamarin a karshen wannan watan da muke ciki.
Facebook Forum