Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: Yaya dangantakar Rasha da Mali da Burkina Faso za ta kasance tunda harsunansu daban, takardar kudinsu ma daban(ii)?


Ibrahim K Garba
Ibrahim K Garba

Yau mun zo ma ku ne da kashi na biyu kuma na karshe na amsar tambaya kan yadda dangantakar Rasha da kasashen Mali da Burkina Faso za ta kasance saboda harsunansu daban, takardun kudinsu ma daban.

Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.

TAMBAYA

Yau za a ji kashi na biyu kuma na karshe na amsar tambayar nan mai cewa, "Assalamu alaikum VOA Hausa. Muna so ku tambaya mana masanan harkokin kasa-da kasa, kan yanda kasar Mali da Burkina Faso ke shirin kulla yarjejeniya da kasar Rasha, maimakon kasar Faranasa. Yaya lamarin zai kasance? Za a dinga koyar da harshen Rashanci a makarantun Bokon kasashen, ko za a cigaba da amfani da harshen Faransanci ne. Kasashen biyu za su dinga amfani da takardar kudin CFA, wadda kasar Faransa ke buga musu ne Ko kuwa?"

Masu Tambaya: Idan an tuna, masu tambayar su ne Babandi Mamman Bande, da Tasiu Unguwar Tudu, Damagaram da Issuhu Madatai, da Ali Sarkin yakin Ni'ma, da shugaba Iliya Maishayi Garkin Daura.

AMSA: To idan masu tambayar, da ma sauran masu sha’awar jin amsar, na tare da mu, ga kashi na biyu kuma na karshe na amsar da wakilin Muryar Amurka a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, ya samo daga wurin Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero da ke Kano, kamar yadda za a ji.

Sai a kasance da mu makon gobe don jin amsoshin wasu tambayoyin.

A yi saurare lafiya:

10-22-22 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:11:47 0:00
XS
SM
MD
LG