Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: Wani tasiri dangantaka tsakanin Rasha da kasashen Mali da Burkina Faso za ta yi kan harshe da takardar kudi?


Ibrahim K Garba
Ibrahim K Garba

Yau mun zo ma ku ne da amsar tambaya kan yadda dangantakar Rasha da kasashen Mali da Burkina Faso za ta kasance ganin cewa takardar kudi daban ne kuma harshe ma daban.

Masu sauraronmu assalama alaikum; barkanmu dasake saduwa a wannan shirin na amsoshintambayoyinku.

TAMBAYA

"Assalama alaikum VOA HAUSA. Muna so ku tambaya mana masanan harkokin kasa-da kasa, kan yanda kasar Mali da Burkina Faso ke shirin kulla yarjejeniya da kasar RASHA, maimakon kasar Faranasa. Yaya lamarin zai kasance? Za a dinga koyar da harshen RASHAnci ne a makarantun Bokon kasashen, ko za a cigaba da amfani da harshen Faransanci ne. Kasashen biyu za su dinga amfani da takardar kudin CFA, wadda kasar Faransa ke buga musu ne Ko kuwa?"

Masu Tambaya: Babandi Mamman Bande, da Tasiu Unguwar Tudu, Damagaram da issuhu Madatai, da Ali Sarkin yakin Ni'ma, da shugaba Iliya Maishayi Garkin Daura.

AMSA: To idan masu tambayar, da ma sauran masu sha’awar jin amsar na tare da mu, ga amsar da wakilin Muryar Amurka a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, ya samo daga wurin PROF. Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero da ke Kano, kamar yadda za a ji a sauti.

Sai a kasance da mu makon gobe don jin kashi na biyu na amsar wannan tambayar da ma amsoshin wasu tambayoyin.

A yi saurare lafiya:

10-15-22- AMSOSHIN TAMBAYOYINKU.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:11:40 0:00
XS
SM
MD
LG