TAMBAYA 1:
Assalamma alaikum, bayan gaisuwa da fatan alkhairi, ga masu gabatar da wannan shirin, ga tambaya da na ke so ku amsa ma ni:
Gameda canjin launin kudi da za ayi a Nigeria, kamar yanda na gani a wasu kafofin yada labarai, ance za a Kashe har N58.21billion wajen buga sababin kudi N2.52billion.To wai idan haka gaskiya ne, me wan nan yake nufi ? Anci riba ko faduwa akayi kenan?
Wassalam Ku huta lafiya.
MAI TAMBAYAR: Dalhatu Manjos Gobir, Samaru Busstop Zaria, Jahar kaduna
TAMBAYA 2:
Assalamma alaikum voa Hausa. Don Allah a kasashenmu na afirka harsuna manya
manya, wadanda muke magana da su, kuma mutane su fahimta, guda nawa ne.
MASU TAMBAYA: Kawu Mairuwa Bajoga, da Alhaji Kari Bage Bajoga.
AMSA 1:
To bari mu fara da tambaya kan batun canjin kudi, idan mai tambaya, Dalhatu Manjos Gobir na tare da mu, ga amsarka da wakilin Sashin Hausa a yankin Adamawa, Muhammad Salisu Garba, ya samo daga Dr Adamu Babikwai malami a kwalejin horas da malamai mallakar gwamnatin Nigeria dake jihar Adamawa wato FCE yola, wanda ya ba da amsa kamar yadda za a ji.
AMSA 2:
Sai kuma maimaicin amsar tambaya kan manyan harsunan da ake amfani da su a Afurka sosai. Idan masu tambayar Kawu Mairuwa Bajoga da alh. Kari Bage na tare da mu, ga amsarku da wakilinmu a Adamawa, Muhammad Salisu Lado ya samo daga Dr. Mahdi Abba, Malami a jami’ar modibbo adama dake yola, jihar Adamawa, Najeriya, wanda ya yi bayani kamar yadda za a ji.
A yi saurare lafiya: