Masu sauraronmu assalamu a laikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku:
Tambaya: Assalamu alaikum VOA Hausa. Bayan gaisuwa da fatan alkhairi ga masu gabatar da wannan shiri; ga tambayata kamar haka: Wai don Allah a wadanne kasashe ne matasa su ka samu damar kama madafun mulki? Matasan sun taka rawar gani a zamanin mulkin nasu? Wasalam ku huta lafiya.
Mai Tambaya: Dalhatu Manjus Gobir, Samaru Bus Stop, Zariya, jihar Kadunan Najeriya.
Amsa: Idan mai tambayar da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, ga kashi na biyu na amsar da wakilin Muryar Amurka a Kaduna, Isa Lawan Ikara, ya samo daga Farfesan Tarihi a Jami’ar ABU Zaria, Dakta Salisu Bala.
A sha bayani lafiya:
Dandalin Mu Tattauna